in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar da Rasha sun sanya hannu kan yarjejeniyar ginin tashar samar da wuta ta makamashin nukiliya
2017-12-12 12:25:21 cri
Kasashen Masar da Rasha sun sanya hannu kan yarjejeniyar ginin tashar samar da lantarki ta makamashin nukiliya a kasar Masar. Ministan ma'aikatar samar da lantaki ta Masar Mohamed Shaker, da shugaban hukumar sarrafa makamashin nukiliya na Rasha Rosatom Alexei Likhachev ne suka sanya hannu kan takardun yarjejeniyar.

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da takwaransa na Rasha dake ziyarar aiki a Masar Vladimir Putin, sun ganewa idanun su sanya hannu kan kwantiragin.

A watan Fabarairun shekarar 2015 ne dai shugabannin kasashen biyu suka sanya hannu kan tushen yarjejeniyar, wadda ta kunshi ginawa Masar tashar samar da lantarki da ke da na'urorin sarrafa nukiliya 4 nan da shekara ta 2022.

A kuma watan Mayun shekarar bara, Masar ta amince da karbar bashin dalar Amurka biliyan 25 daga Rasha domin aiwatar da ginin cibiyoyin.

Karkashin tsarin yarjejeniyar dai, Moscow za ta samar da kaso 80 bisa dari na nau'o'in kayayyakin da ake bukata, yayin da kuma Masar za ta samar da kaso 20 bisa dari domin gudanar aiki.

Za a kafa tashar ne a birnin Dabaa dake lardin Matrouh mai iyaka da teku.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China