Da yake tabbatar da hakan, jagoran tafiyar, kuma shugaban jam'iyyar Nation's Future Party a kasar Mohamed al-Garhy, ya bayyanawa wani taron 'yan jaridu cewa, kawo yanzu sun riga sun tattara sanya hannu na al'ummar kasar 12,132,640 tsakanin watan Satumbar da ya gabata zuwa yanzu.
Mr. Al-Garhy, ya kara da cewa, babban muradin su shi ne tabbatar da nasarar shugaban mai ci yayin babban zaben kasar dake tafe, duba da yadda shugaban na Masar ya jajirce, wajen dakile mummunan yanayin siyasa da ya aukawa kasashen larabawa mai cike da tashe tashen hankula, musamman kasashen Syria, da Libya da kuma Yemen.