Hukumar kula da dokokin hanya ta ma'aikatar, ta bayyana a jiya cewa, jimilar ababen hawa 825,000 ne ke amfani da lantarki, yayin da 193 ke amfani da lantarki da ake hadawa da sassa daban-daban na fasahohi.
Domin gane wadannan motoci, ma'aikatar MPS ta ware wasu birane 5, inda a cikinsu aka rarraba lambar mota ta musamman ga masu amfani da makamshi mai tsafta a bara.
Lambobin za su mamaye dukkan biranen kasar Sin zuwa rabin farko na shekarar 2018.
A cewar ma'aikatar, ana sa ran yawan ababen hawa masu aiki da makamashi mai tsafta kerawa tare da sayarwa, ya zarce miliyan 5 zuwa shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)