Rahoton hukumar na shekara-shekara da aka wallafa a jiya Laraba ya ce, an samu karuwar bukatar 'yancin mallakar fasaha a bangarorin masana'atu a duniya ne a shekarar 2016, biyo bayan karuwar wannan bukata a kasar Sin.
Bugu da kari rahoton ya ce, kasar Sin ta karbi takardun masu neman 'yancin mallakar fasaha kimanin 236,600 baya ga kamfanoni 240,600 da suka gabatar da wannan bukata, adadin da ya karu da kaso 98 cikin 100.
Da yake yiwa maname labarai karin haske, darektan hukumar ta WIPO Francis Gurry, ya ce sabbin alkaluma sun nuna tsawon lokacin da aka dauka na karuwar masu bukatar 'yancin mallakar fasaha, kuma kasar Sin ce ke sahun gaba a duniya a wannan fanni.
Haka kuma, kasar ta Sin tana kara zama a kan gaba a fannin kirkire-kirkire da tambarin kayayyaki a duniya.(Ibrahim)