in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar firaministan Sin ta gana da masanan ketare
2018-01-09 10:07:01 cri
A jiya Litinin ne mataimakiyar firaminsitan kasar Sin Liu Yandong ta gana da masanan kasashen ketare, wadanda suka sami lambobin yabo na hadin gwiwar kimiyya da fasahar kasa da kasa, na jamhuriyyar jama'ar kasa ta Sin na shekarar 2017.

Wadannan masana sun hada da masanin ilmin aikin kira na kasar Amurka Earl Ward Plummer, da masani a fannin kimiyyar halittu na kasar Uzbekistan Salikhov Shavkat, da masani mai nazari ilmin aikin kira na kasar Amurka Shoucheng Zhang, da masani kan kimiyyar polymer na kasar Burtaniya Philip David Coates. Sauran sun hada da masanin yanayi na kasar Sweden Deliang Chen, da masanin ilmin gadon kwayoyin halitta na kasar Amurka Yang Shi da kuma masani kan ilmin injiniyancin gine-gine na kasar Amurka Polichronis-Thomas Spanos.

Liu Yandong ta taya masanan murnar cimma lambobin yabo, ta kuma godewa wadannan masana, bisa babbar gudummawa da suka bayar wajen raya kimiyya da fasahar kasar Sin, da kuma ci gaban zamantakewar al'ummomin kasashen duniya baki daya.

Haka kuma, ta ce, kasar Sin za ta dukufa wajen inganta hadin gwiwar kasa da kasa domin neman bunkasuwar kimiyya da fasaha, da kuma samar da kyawawan damammaki ga masanan kasashen ketare, wadanda ke zuwa kasar Sin don gudanar da ayyukansu, da kuma yin shawarwari da masanan kasar Sin abokan aikin su.

Bugu da kari, tana fatan masanan kasar Sin da masanan kasashen ketare za su iya karfafa mu'amalar dake tsakaninsu, ta yadda za a fuskanci kalubaloli cikin hadin gwiwa, yayin da ake ba da sabuwar gudummawa ga dunkulewar al'ummomin kasa da kasa.

Tun daga shekarar 1995 ya zuwa yanzu, gaba daya akwai masanan ketare guda 113, da kuma kungiyoyin kasa da kasa guda 3, wadanda suka cimma nasarar samun lambobin yabo na hadin gwiwar kimiyya da fasaha na kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China