Babban injiniyan kamfanin CRRC Qu Tianwei ya bayyana cewa, tun a cikin shekaru takwas da suka gabata ne kamfanin ya fara gudanar da bincike game da kera sabon jirgin na Maglev. Kuma gwajin gudun da jirgin ya yi ya nuna ci gaban da kasar Sin take da shi a fasahar kera sabon jirgin kasa na Maglev.
Mr Qu, ya kara da cewa, idan aka kwatanta da tsohon tsarin jiragen kasa, sabon jirgin kasa mai matsakaici da karamin gudu na zamani, ba shi da kara sosai, kana yana da inganci matuka.
A watan Mayun shekarar 2016 da ta gabata ce dai jirgin kasa na Maglev na kasar Sin na farko ya fara aiki a birnin Changsha dake lardin Hunan a tsakiyar kasar Sin, lamarin da ya sanya kasar Sin zama kasa ta farko a duniya da ta lakanci wannan fasaha.
Rahotanni na nuna cewa, kudaden da aka kashe wajen gina layukan jirgin na Maglev sun dara layukan jiragen zamani dake zirga-zirga tsakanin manyan biranen kasar, amma ba su kai na layukan jiragen karkashin kasa ba. (Ibrahim Yaya)