Shugaba Xi ya ce, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa da bangarorin kimiyya da fasaha da masana'antu na kasa da kasa, domin inganta ayyukan yin nazari da sarrafa mutum-mutumin inji, ta yadda za a ci gajiyar fasahohin mutum-mutumin inji wajen neman bunkasuwa da kuma tallafawa al'ummomin kasa da kasa.
Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya mika sakon taya murna ga taron, inda ya yi fatan masana da masu kamfanoni na kasa da kasa za su yi hadin gwiwa wajen inganta fasahar mutum-mutumin inji da kuma ciyar da ayyukan dake shafar kimiyya da fasahar mutum-mutumin inji gaba, ta yadda za a bullo da sabbin hanyoyin raya tattalin arzikin duniya da kuma ba da gudummawa yadda ya kamata a yayin da aka shiga wani zamani na amfani da fasahar kere-kere. (Maryam)