A jawabinsa yayin bikin mika cibiyar, Liu Xianfa ya bayyana cewa, cibiyar nazari ta hadin gwiwar Sin da Afirka, ita ce babbar hukumar nazari da samar da ilmi ta farko da gwamnatin kasar Sin ta gina a ketare, kuma ta kasance babbar alama ta hadin gwiwa da musaya tsakanin kasar Kenya da kasar Sin. Ya ce, yana fatan kasashen biyu za su karfafa fahimtar juna a tsakaninsu ta hanyar yin hadin gwiwa a fannin nazari, a kokarin neman ci gaba tare.
Mataimakiyar shugaban jami'ar kimiyya da fasahar noma ta Jomo Kenyatta Mabel Imbuga ta nuna godiya matuka dangane da taimakon da gwamantin Sin ta samar wa jami'ar. Ta kuma bayyana godiya matuka da fasahohin zamani da sahihiyar kawar Sin ta kawo wa kasar Kenya, inda aka gina wannan cibiyar nazari ta hadin gwiwar Sin da Afirka, tare samar da horo ta fuskar kimiyya da fasaha ga 'yan kasar, lamarin da zai samar da dama mai kyau ga kasashen biyu wajen karfafa hadin gwiwarsu a fannin yin nazari a nan gaba. Ta ci gaba da cewa, cibiyar nazarin za ta tallafa wa kasar Kenya, har ma ga dukkan kasashen Afirka baki daya. (Maryam)