in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama wajibi Afirka ta mai da hankali ga kimiyya da fasaha
2016-08-24 10:49:01 cri

Masana daga sassan nahiyar Afirka dake taron karawa juna sani, game da harkokin kimiyya da fasaha a birnin Kigalin kasar Rwanda, sun yi kira ga mahukuntan kasashen nahiyar da su mai da hankali ga bunkasa wannan fannoni na ilimi, a wani mataki na fidda Afirka daga kangin da take ciki.

Yayin taron na shekara shekara, masanan sun bayyana cewa, raya sha'anin kimiyya da fasaha zai ba da damar kakkabe talauci, tare da ba da damar cimma nasarar kudurorin ci gaba na shekarar 2063.

Da take tsokaci game da hakan, babbar sakatariya a cibiyar raya kimiyya da fasaha ta gabashin Afirka Gertrude Ngabirano, ta ce, Afirka na bukatar zuba jari a wadannan fannoni domin sauya alkiblar tattalin arzikin ta.

Kasar Rwanda ce ke karbar bakuncin taron na bana, wanda zai gudana tsakanin ranekun 22 zuwa 26 ga watan nan, bisa taken "kimiyya da fasaha, da tasirin su a fagen bunkasa tattalin arziki, a shiyya shiyya tare da samar da ci gaba mai dorewa".

Kaza lika taron zai baiwa mahalartan sa damar tattauna batutuwa daban daban a matsayin hanyar musayar ilimi, da zakulo hanyoyin sauya akalar nahiyar Afirka, don samun ci gaba ta hanyar amfani da dabaru na kimiyya da fasaha.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China