An cimma wannan matsaya ne a lokacin zaman majalisar gudanar da sha'anin mulki, wanda firaiminsta Li Keqiang ya jagoranta a ranar Laraba, a lokacin da aka gabatar da rahoton aiwatar da wannan shiri ga masu ruwa da tsaki.
Tun lokacin da aka aiwatar da shirin a shekarar 2015, kasar Sin ta ga nasarori masu yawa da aka samu ta fuskar karfin masana'antun kasar, da amfani da fasahohin zamani, da kirkire kirkire, da samar da kayayyaki masu inganci. Ci gaban da aka samu na baya bayan nan shi ne na kera jirgin saman fasinja samfurin C919 wanda ya tashi da fasinjoji a karon farko a matsayin gwaji a cikin wannan wata da muke ciki.
Taron majalisar ya yanke shawarar mayar da hankali kan zamanantar da masana'antu da kuma shigar da sabbin fasahohin zamani kamar yin mafani da na'urorin intanet domin saukaka aikin da masana'antun ke gudanarwa, da tafiyar da aikin cikin sauri, da samar da ingancin kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa, ko kuma suke gudanarwa na ayyukan bada hidima.
Ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, an samu ingancin ayyukan masana'antun kasar da kashi 38 bisa 100 cikin wasu ayyukan gwaji kimanin 109 da aka gudanar, kana an samu saukin kashe kudi da kashi 21 bisa 100 sakamakon amfani da sabbin manufofin.
Firaiministan ya ce shirin na "Made in China 2025", wani muhimmin bangare ne da zai tabbatar da yin garam bawul a fannin, da kuma kara samun bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. (Saminu Hassan)