in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta sanya ranar zabukan Shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki
2017-12-25 10:47:48 cri
Shugaban hukumar zaben Kasar Libya Imad al-Sayeh, ya tabbatar a jiya cewa, zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar za su gudana kafin ranar 30 ga watan Satumban badi.

Imad Al-Sayeh ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, aikin yi wa masu zabe rejista na gudana yadda ya kamata, inda ya ce kawo yanzu an yi wa mutane miliyan 1 rejista, inda kuma adadin ke kara karuwa.

A cikin watan Satumban da ya gabata ne shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libya, ya gabatar da wani shirin na kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Shirin ya kunshi yi wa yarjejeniyar siyasar kasar na yanzu gyaran fuska, tare da gudanar da zabukan 'yan majalisu da na Shugaban kasa.

A baya bayn nan, Tunisia ta karbi bakuncin wani taro da MDD ta dauki nauyi, wanda ya gudana tsakanin wakilan jam'iyyun siyasar Libya, da nufin gabatar da gyaran fuska kan yarjejeniyar.

Tun bayan rikicin 2011 da ya hambarar da mulkin Gaddafi, Libya ke ta kokarin sauya mulki inda ake tsaka da fuskantar rikici da rarrabuwar kawuna a sanadin siyasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China