Ya kuma kara da cewa, cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta sassauta saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, domin tabbatar da ci gaba na bunkasuwar tattalin arzikin yadda ya kamata, kuma cikin yanayi mai kyau.
Haka zalika, bisa fasahohin da aka samu cikin tarihi dangane da bunkasuwar tattalin arziki, an ce, ko wace sana'a tana ba da muhimmiyar gudummawa, wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Shi ya sa, kasar Sin ke neman dauwamammen ci gaban tattalin arzikinta, tare da mai da hankali kan bunkasuwar dukkan sana'o'in masu alaka da hakan.
Bugu da kari, Mr. Carroll ya bayyana cewa, kasar Sin tana da burinta, na kandagarki, da kuma warware manyan kalubalolin dake gabanta, musamman ma a fannin sha'anin kudi, da kawar da talauci da kuma kiyaye muhalli, idan kasar ta cimma nasarori a wadannan fannoni, tabbas za ta ba da muhimman darussa ga sauran kasashen duniya. (Maryam)