in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kudin Sudan: Tattalin arzikin Sudan na fuskantar kalubalen da za a iya shawo kan su bisa daukar wasu matakai
2018-01-03 10:36:17 cri

Ministan kudin Sudan Mohammed Osman Al-Rikabi, ya ce tattalin arzikin kasarsa na fuskantar kalubale, amma za a iya shawo kansu ta hanyar daukar dabaru da matakai.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Mohammed Al-Rikabi, ya ce daya daga cikin kalubalen da Sudan ke fuskanta shi ne, faduwar darajar takardar kudinta na Pound da kuma hauhawar farashin muhimman kayayyaki.

Ministan ya kuma kare kasafin kudin kasar na bana, wanda majalisar ministocin kasar ta amince da shi cikin watan Disamban da ya gabata, sannan majalisar dokokin kasar ta mayar da shi doka a ranar 31 ga watan na Disamban.

Ya kuma bayyana wahalar samun kudade saboda zargin da ake wa kasar na daukar nauyin 'yan ta'adda da gibin da ake samu wajen cinikayya a matsayin karin kalubale.

Ministan kudin ya kuma jaddada cewa, har yanzu kasarsa ba ta fara cin moriyar dage takunkumin tattalin arzikin Amurka ba, yana mai cewa za a dauki lokaci kafin a fara ganin tasirin matakin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China