Duk a cikin wannan rahoton, an yi hasashen ganin alamar karuwa a dukkanin bangarorin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, gami da samar da kayayyaki, a shekarar 2018 dake tafe, sai dai kar a yi biris da wani yanayi na rashin tabbas da hadarin dake tare da shi. An ce, wannan yanayi na rashin tabbas yana kalubalantar tattalin arzikin kasar Sin, amma a sa'i daya, yana samar da damammaki ga kasar Sin don kara raya tattalin arzikinta.
A cewar rahoton, matakan da kasar Sin za ta iya dauka don tinkarar wannan yanayi sun hada da, ci gaba da gudanar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" don daidaita tsarin tattalin arzikin duniya, da kyautata manufar diplomasiyyarta don kara kulla huldar hadin gwiwa da sauran kasashe, da kara bude kofarta don taimakawa yada wannan manufa a duniya, gami da kokarin samar da kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin al'ummomin duniya.(Bello Wang)