Rahoton ya ce, a nan gaba, kasar Sin za ta kara nuna kwazo wajen aiwatar da manufofin kudi da na tattalin arziki gadan-gadan, kana, za ta yi iyakar kokarin shawo kan hadarurran da za su iya kunno kai da tallafawa mutanen dake fama da talauci da daidaita matsalar gurbacewar muhallin halittu da kuma yin kwaskwarima a wasu manyan fannoni. Rahoton ya yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da bunkasa da kyau kuma yadda ya kamata.(Murtala Zhang)