Cikin sakon sa na bikin kirsimeti ga al'ummar kasar, Mr. Ramaphosa ya ce ya zama wajibi al'ummar kasar su yi aiki tare, wajen farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar kau da dukkanin shingaye, dake yiwa harkokin zuba jari tarnaki, tare da tabbatar da ci gaban kasar yadda ya kamata.
Ya ce duk da tarin irin ci gaba da aka samu a sassa daban daban a shekarar nan ta 2017, matsalolin karancin guraben ayyukan yi tsakanin al'ummar Afirka ta kudu na cikin matsaloli dake addabar kasar. Don haka ya yi kira ga al'ummar kasar, da su dukufa wajen ginin kasa ta hanyar marawa shirin samar da ci gaban kasar baya.
Mr. Ramaphosa ya kara da cewa, karkashin wannan tsari na bunkasa Afirka ta kudu, an tanaji matakai na samar da ci gaba a dukkanin sassa, da kyautata zamantakewar al'umma nan da shekarar 2030, yayin da kasar ke kara samar da dabarun cimma burikan ta na wadata, da biyan bukatun da suka shafi kwadago.