in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An fidda alkaluman farko na ma'aunin tattalin arziki mai nasaba da kyautata muhalli
2017-12-26 15:40:57 cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS a takaice, ta fidda wasu alkaluma irin su na farko, wadanda ke iya nuna matsayin ci gaban tattalin arzikin kasar mai nasaba da kyautatuwar muhalli.

Rahotanni sun nuna cewa, alkaluman sun kunshi ma'aunai 55, ciki hadda masu alaka da kyautata amfani da makamashi, da na fidda hayaki mai tattare da sinadarin carbon, da ingancin iska da ake shaka. Sauran sun hada da yawan kudaden kashewa dake hannun mutane, da wadanda ake warewa domin gudanar da bincike da samar da ci gaba.

Fidda alkaluman awon na "green development index" a turance, na zuwa ne shekara guda, tun bayan da mahukuntan kasar suka amince da amfani da su wajen auna kwazon kananan hukumomi, game da kare ko kyautata yanayin muhalli da bunkasa muhallin halittu.

Kaza lika hakan zai kasance ma'aunin daukaka matsayin jami'an dake aiki a kananan hukumomin, da ma horo ga wadanda aka kama da aikata laifuka, a gabar da kasar ta Sin ke kara maida hankali ga ci gaba mai nagarta.

A makon da ya gabata ne dai aka fitar da wani rahoton bayan taron koli, game da tattalin arzikin kasar ta Sin mai nasaba da tattalin arziki, wanda ke nuni ga yadda ci gaban kasar ya shiga wani sabon zamani, mai tattare da sauyi daga saurin bunkasa zuwa ci gaba mai nagarta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China