A halin yanzu, akwai kimanin jiragen saman na MA60 14 wadanda ke gudanar da ayyukan jigila a kasashen tsakiyar Afrika 7, wanda ya hade hanyoyin zirga-zirgar jiragen saman na shiyyoyi 20, wanda hakan ya taimaka wajen hade yankuna masu yawa ta hanyar sufurin jiragen sama a shiyyar.
Kamfanin kula da harkokin sufurin jiragen sama mallakar kasar Sin (AVIC), ya sanar da cewa kamfanin Aero-Development Corporation na kasa da kasa, wanda wani bangare ne na AVIC, yana gudanar da ayyuka masu yawa da suka hada da tafiyar da harkokin zirga zirgar jiragen sama tsakanin kasar Sin da shiyyar Afrika.
Domin tabbatar da gudanar da harkokin sufurin kananan jiragen saman tsakanin kasar Sin da Afrika, AVIC International ya kafa tsarin kasuwanci da ya hade sassan da kuma biyan muradun abokan huldar kamfanin kananan jiragen saman kirar kasar Sin tsakaninsu da kasashen na Afrika.
Kamfanin kananan jiragen saman kirar kasar Sin yana gudanar da harkokin sufuri a kasashen dake magana da harsunan Turanci da Faransanci a shiyyoyin na Afrika. (Ahmad Fagam)