Darektan sashi mai kula da aikin soja da harkar tsaro a ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin mista Wang Qun, ya jagoranci wata tawagar jami'an kasar Sin zuwa taron.
A jawabin sa, mista Wang ya jaddada matsayin da kasar Sin ta dauka na goyon bayan yarjejeniyar da aka kulla kan batun nukiliyar kasar Iran. A ganin kasar Sin, yadda ake kokarin aiwatar da yarjejeniyar, yana da ma'ana sosai ga yunkurin hana bazuwar makaman kare dangi, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a gabas ta tsakiya, don haka ya dace da moriyar bai daya ta gamayyar kasa da kasa.
A cewar jami'in na kasar Sin, kamata ya yi, kasashe 6 masu ruwa da tsaki, gami da kasar ta Iran, su ci gaba da kokarin cika alkawuran da suka yi, na tabbatar da matsayin yarjejeniyar. Haka zalika, ana bukatar su tabbatar da amincewar juna bisa kokarin gudanar da yarjejeniyar da aka kulla, gami da shawo kan sabanin ra'ayin da aka samu. (Bello Wang)