in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Layin jirgin kasa na zamani da kasar Sin ta gina daga Habasha zuwa Djibouti ya fara aiki
2018-01-02 11:03:49 cri
Aikin layin dogo mai amfani da lantarki mai nisan kilomita 756 wanda ya tashi daga kasar Habasha zuwa Djibouti ya fara aiki a ranar Litinin, inda aka gudanar da bikin bude shi a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Da yake jawabi a lokacin bikin, ministan sufurin kasar Habasha Ahmed Shide, ya yaba da ingancin aikin, inda ya bayyana shi da cewa ya kasance a matsayin wani muhimmin cigaba da aka samu dangane da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika.

Baya ga karfafa kyakkyawar mu'amalar tattalin arziki, da kyautata cudanya tsakanin al'ummomin kasashen Habasha da Djibouti, aikin zai kara bada gudunmowa wajen gina sabon cigaban kasar ta Habasha, inji ministan.

Ministan ya yabawa kasar Sin da kuma dukkan masu ruwa da tsaki da suka bada gudunmowa wajen samun nasarar gudanar da aikin layin dogon, kana ya bukaci al'ummar kasar, musamman mazauna yankunan dake daura da layin dogon da su bada kyakkyawar kulawa don tabbatar da ganin aikin ya samu dorewa yadda ya kamata.

A nasa bangaren, jakadan Djibouti a kasar Habasha, Mohamed Idriss Farah, ya bayyana cewa, aikin layin dogon zai kara habaka cigaban tattalin arzikin kasashen Djibouti da Habasha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China