in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha: Za a kaddamar da yankin masana'antun harhada magunguna a watan Maris
2017-12-25 09:52:27 cri
Kasar Habasha za ta fara cin gajiya daga wani katafaren yankin harhada magunguna da ake ginawa a Kilinto tun daga watan Maris na shekarar 2018.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya, jagoran aikin ginin yankin masana'antun Getahun Agenew, ya ce ya zuwa yanzu an kammala kaso kusan 75 bisa dari na aikin.

Kamfanin gine gine na kasar Sin mai suna Tiesiju ne dai ke gudanar da wannan aiki, wanda kuma zai mamaye filin da ya kai hekta 270, za kuma a kammala shi kan kudi har dalar Amurka miliyan 204.

Rahotanni sun bayyana cewa, babban bankin duniya ne ya samar da rancen kudaden gudanar da wannan muhimmin aiki.

Yankin masana'antun na Kilinto, zai kunshi hanyoyin mota da suka kai tsawon kilomita 18, da sauran abubuwan da al'umma za su bukata na amfanin yau da kullum, da wuraren shan iska da na ajiyar kayayyaki. Sauran sun hada da wuraren hada hadar cinikayya da na ajiyar motoci.

Kawo yanzu an kaddamar ko ana kan ginin jimillar yankunan masana'antu 15 a kasar ta Habasha, a wani mataki na maida kasar babbar cibiyar masana'antu ta nahiyar Afirka nan da shekara ta 2020.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China