in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta sanar da mutuwar mutane 78 a tashin hankali tsakanin Oromo da Somali
2017-12-20 11:01:16 cri

Mahukuntan kasar Habasha sun ce, an hallaka mutane a kalla 78 a wani tashin hankali na baya-bayan nan da ya barke a tsakanin 'yan kabilun Oromo da Somali.

Jami'i mai kula da al'amuran hukumar sadarwar kasar Habasha Negeri Lencho, ya bayyana cewa, tashin hankali wanda ya afku a ranar 14 ga watan Disamba a yankunan Hawi Godina da Daro Labo dake yammacin shiyyar Hararghe na jahar Oromia, sakamakon mutuwar wani fitaccen mutum, dan kabilar Oromo.

Lencho, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a ranar 14 ga watan Disambar, a lokacin da 'yan kabilar Oromo ke kan hanyarsu ta dawowa daga karbar kayan tallafin abinci, wasu 'yan bindiga suka yi musu kwanton bauna, wadanda ake kyautata zaton sun fito ne daga wasu kauyuka na 'yan kabilun Somali, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 29.

Musayar wutar da aka samu ya haddasa kone daruruwan gidaje da kuma sace kayan tallafin abincin. Yankin dai ya sha fama da matsanancin fari.

Lencho ya ce, dangin wani fitaccen mutumin da aka kashe a lokacin tashin hankalin sun dauki fansa, inda suka kashe 'yan kabilar Somali 49 wadanda ke zaune a yankunan da ke makwabta.

Ya ce, a halin yanzu gwamnatin tana aiki tare da wasu shugabannin addinai da dattawan yankunan da kuma wasu jami'an yankunan domin warware takaddamar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China