in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha na duba iyuwar inganta dangantaka da kasar Sin
2017-12-22 10:13:14 cri
Gwamnatin Habasha ta bukaci taro kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da al'adu dake gudana tsakaninta da kasar Sin, ya samar da sabbin dabaru masu karfi da za su kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

An bude taron dake gudana a birnin Hangzhou na gabashin kasar Sin ne a ranar Laraba da ta gabata

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Habasha, taron wani muhimmin sakamako ne na daddadiyar alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Aklilu Hailemichael, da ya bayyana daddadiyar dangantaka mai karfi dake tsakanin kasashen biyu da buri iri guda da suke da shi na hadin gwiwa kan bangarorin daban-daban, ya yabawa gwamnati da al'ummar kasar Sin kan rawar da suka taka wajen bunkasa tattalin arzikin kasarsa.

Ya kuma jaddada bukatar inganta tsare-tsaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, tare da ci gaba da raya dangantaka bisa manufofin dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika da na kasashe masu tasowa wato G-77 da sauransu.

Aklilu Hailemichael, ya kuma yi wa mahalarta taron bayani game da albarkatun da kasar ke da su da ba a amfana da su, da kuma kudurin gwamnatin na inganta shirye-shiryen zuba jari a kasar dake gabashin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China