Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook, Ofishin Firaministan kasar Hailemariam Desalegn ya ce za a rufe cibiyar tsare mutane na Maekalwi dake birnin Addis Ababa.
Sanarwa dai ba ta yi karin haske game da wadanda za a saki da kuma lokacin rufe cibiyar ba.
Magoya bayan bangaren adawa da masu zanga-zanga na zargin Gwamnatin kasar da amfani da cibiyar tsare mutanen wajen tilastawa wadanda ake zargi amsa laifi, inda ake tuhumarsu karkashin dokar da ta haramta ta'addanci.
Habasha ta fuskanci tashin hankali a shekarar 2016 da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, wanda masana suka bayyana a matsayin babban kalubalen da jam'iyyar kawance ta Ethiopian Peoples Revolutinary Democratic Front ta fuskanta cikin shekaru 25. (Fa'iza Mustapha)