Babbar darektar ta bayyana cewa, masana'antun kasar Sin sun samar da dimbin guraben aikin yi a kasar Habasha, sun kuma kyautata kwarewar ma'aikatan wurin, abin da ya taimaka matuka ga samun dauwamammen ci gaban harkokin cinikayya da kasar ta Habasha ke yi da kasashen waje, da kuma sauyin tsarin tattalin arzikin kasar.(Lubabatu)