An dai kaddamar da matakan sojin ne tun daga ranar 15 ga watan Nuwamba, yayin da a yanzu haka dukkan dakarun rundunar sojoji da ta 'yan sandan kasar suka koma gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba.
A yayin taron manema labaran da rundunar sojojin kasar ta kira a ranar 18 ga wata, sabon kwamandan rundunar Rhilip Valerio Sibanda ya bayyana cewa, an riga an cimma burin daukar matakan soja, an gurfanar da wasu masu laifuffuka gaban kuliya, yayin da wasu suka tsere kasashen ketare.
Haka kuma, ya yi kira ga sojoji da 'yan sandan kasar da su yi hadin gwiwa wajen gudanar da ayyuka bisa dokokin kasar yadda ya kamata, domin kawar da cin hanci da karbar rashawa baki daya a duk fadin kasar, ta yadda za su ba da gudummawa ga bunkasuwar kasar ta Zimbabwe.
Daga bisani kuma, gwamnatin kasar Zimbabwe ta fidda wata sanarwa a jiya Litinin, inda ta sanar da cewa, janar Constantine Chiwenga wanda ya kaddamar da matakan soja a wannan karo ya riga ya yi ritaya, kuma an cire shi daga matsayin kwamandan rundunar sojojin kasa. Kana, za a mai da shi wani matsayi na daban a nan gaba. (Maryam)