in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zimbabwe zai kai ziyarsarsa ta farko zuwa ketare
2017-12-21 10:56:48 cri
A yau Alhamis ne ake sa ran shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa zai kai ziyara kasar Afirka ta kudu, ziyararsa ta farko zuwa kasashen wajen tun bayan aka rantsar da shi a watan da ya gabata.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Bongani Ngqulunga ya bayyana cewa,a ranar Alhamis ne shugaban Mnangagwa zai ziyarci takwaransa na Afirka ta kudu Jacob Zuma a birnin Pretoria,inda ake sa ran za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasa da kasa da yankuna da kuma shiyya-shiyya.

Wasu rahotanni daga ofishin jakadancin Zimbabwe dake kasar Afirka ta kudu na cewa, ana sa ran shugaba Mnangagwa zai yi amfani da wannan ziyara wajen janyo masu sha'awar zuba jari daga Afirka ta kudu kan yadda za su zuba jari a kasarsa. Haka kuma jami'an gwamnatin kasar ta Zimbabwe za su gana da 'yan kasuwar Afirka ta kudu a yayin wannan ziyara.

Bayanai na nuna cewa, tun zamanin gwagwarmayar kwatar 'yanci kasashen Afirka ta kudu da Zimbabwe suke hulda da juna a fannin siyasa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China