in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe yace kasar za ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2018
2017-12-21 10:37:22 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya nanata aniyar gwamnatinsa cewa za ta yi dukkan abin da ya dace don tabbatar da ganin ta aiwatar da sahihin zabe mai tsabta a kasar.

Da yake jawabin bude taron hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar a karon farko tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar ta Zimbabwe a ranar 24 ga watan Nuwamba, Mnangagwa ya ayyana aniyar gwamnatinsa na gina ingantaccen tsarin mulkin demokaradiyya a kasar.

Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta karfafa mulkin demokaradiyya ta hanyar mutunta tsarin mulkin kasar, da dokokin kasa, da sauraron ra'ayoyin 'yan kasar, da tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Shugaban ya kara da cewa, gwamnatinsa ba za ta laminci aikata rashawa ba, don ta haka ne za ta samu nasarar bunkasa tattalin arzikin kasar.

A cewar shugaban kasar, matsalolin cin hanci da rashawa su ne manya abubuwan da suka jefa kasar cikin halin karayar tattalin arziki da take fama da shi.

Ya ce bunkasuwar tattalin arziki yana bukatar gwamnati mai tsabta, da hukumomi masu zaman kansu masu tsabta. Ya ce manufar gwamnatinsa shi ne gina sabuwar kasar Zimbabwe, bisa tsarin gwamnati a bude, da shugabanci na gari da yin aiki tukuru, ya ce yana da kyakkyawar fata a shekara mai zuwa kasar zata samu habakar fannin aikin gona da ma'adanai.

Shugaban na Zimbabwe ya gargadi masu aikata fasa kwaurin ma'adanai a kasar, ya ce gwamnati zata tsaurara dokokin kula da kan iyakokin kasar don kaucewa fasa kwaurin, kana zata hukunta wadanda ke da hannu wajen yin almundahanar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China