in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya gana da tawagar JKS
2017-12-17 12:36:47 cri

Shugaban jam'iyyar ZANU-PF, kuma shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya gana da wakiliyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma mataimakiyar shugaban sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS madam Xu Lvping da 'yan tawagarta a birnin Harare a ranar 15 ga wata.

A yayin ganawar, shugaba Mnangagwa ya yi maraba da kuma nuna godiya ga JKS data tura tawagar zuwa taron wakilan jam'iyyar ZANU-PF na musamman. Ya kuma yaba game da irin dankon zumunta dake tsakanin Zimbabwe da Sin a koda yaushe. Shugaban na Zimbabwe ya yi maraba da kasar Sin wajen zuba jari a kasarsa, a kokarin taimakawa kasar don farfado da tattalin arzikinta.

A nata bangaren, madam Xu ta ce, Sin da Zimbabwe na fuskantar sabuwar dama wajen raya huldar dake tsakaninsu. Kasar Sin na son cigaba da zurfafa hadin gwiwa da Zimbabwe a sassa daban daban, da aiwatar da sakamakon da aka samu daga ziyarar shugaba Xi Jinping a Zimbabwe da kuma taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, a kokarin kawowa jama'ar kasashen 2 alheri.

Har ila yau, madam Xu ta halarci taron wakilan jam'iyyar ZANU-PF na musamman, inda ta karanta wasikar murna da kwamitin tsakiya na JKS ya aika da shi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China