in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Iran tana aiwatar da shirin dakatar da kera makaman nukiliya
2017-11-24 09:34:11 cri
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta MDD (IAEA) ta sanar a jiya Alhamis cewa, kasar Iran tana aiwatar da yarjejeniyar dakatar da shirinta mai alaka da makamashin nukiliya.

Babban daraktan hukumar ta IAEA Yukiya Amano, ya fadawa taron manema labarai cewa, ba shine keda alhakin yanke hukunci kan Iran ba idan Tehran din ta gaza aiwatar da yarjejeniyar shirin yin amfani da makamashin nukiliyarta.

Hukumar ta IAEA tana cigaba da bibiyar aiwatar da shirin dakatar da yin amfani da makamashin nukiliyar ta Iran mai cike da tarihi wanda aka cimma matsaya a kai a Vienna a shekarar 2015, karkashin wata cikakkiyar yarjejeniyar da aka tsara wato (JCPOA).

Karkashin wannan yarjejeniyar, Iran ta amince ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliyar domin a sassauta mata takunkumin da kasa da kasa suka kakaba mata.

Tun da farko, Amano ya fadawa taron masu ruwa da tsaki a Vienna cewa, ya zuwa wannan lokaci, hukumarsa ta samu nasarar shiga dukkannin wuraren da take bukata a Tehran.

A cewarsa, IAEA zata cigaba da tantancewa da kuma bibiyar yadda Iran din zata aiwatar da batutuwan da suka shafi cikakkiyar yarjejeniar da aka cimma da ita.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China