Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin na maraba da shirin Koriya ta Arewa, da Koriya ta Kudu na kyautata hadin kansu.
Kalaman na Mr. Geng Shuang na zuwa ne bayan da a jiya Laraba, an bude kafar kauyen Panmunjom, matakin da ake ganin zai iya ba da damar baiwa tawagar Koriya ta Arewan damar halartar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a yi a birnin PyeongChang na Koriya ta Kudu.
Kakakin na ma'aikatar harkokin wajen Sin ya kara da cewa, kasarsa na fatan kasashen duniya za su tallafawa aniyar sassan biyu, bisa burinsu na kau da halin dar dar, da kuma sake amincewa juna tsakanin kasashen makwaftan juna.
Mr. Geng ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na rana rana da ya gudana a Laraba. (Saminu)