Kwanan baya, tsohon wakilin kasar Amurka mai kula da shawarwarin batun nukiliyar zirin Koriya Robert Gallucci ya shawarci kasashen Amurka da Koriya ta Arewa da su yi la'akari da shawarar kasar Sin wato dakatar da ayyukan nukiliya da makamai masu linzami da kuma dakatar da manyan atisayen soja, a kokarin komawa kan teburin shawarwari.
Dangane da lamarin, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su yi la'akari da shawarar da ta gabatar sosai, don ganin sun fitar da zirin Koriya daga halin kaka-ni-ka-yi na nuna wa juna kiyayya a yanzu, ta yadda za a samar da tartibin sharadi da yanayin maido da shawarwari a tsakaninsu. (Tasallah Yuan)