Yau Talata ne a nan Beijing, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana amincewa da kuma goyon bayan kasashen Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa su kyautata huldarsu ta hanyar tattaunawa, kara azama kan samun sulhuntawa da yin hadin gwiwa, a kokarin taka rawa wajen sassauta tashin hanhali a zirin, kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin.
A jiya ne madam Kyung-wha Kang, ministar harkokin wajen kasar Koriya ta Kudu ta ce, kamata ya yi a tuntubi Koriya ta Arewa kana a sanar da ita kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi mata, inda suka bukace da ta yi watsi da shirinta na nukiliya. Gwamnatin Koriya ta Kudu ta shirya tuntubar Koriya ta Arewa, a kokarin ganin ta kyautata hulda a tsakaninta da Koriya ta Arewa. (Tasallah Yuan)