Yau Laraba ne a nan Beijing, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar Sin na fatan kasashen Amurka da Koriya ta Arewa za su ci gaba da tuntubar juna.
Rahotanni na cewa, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki game da manufofin gudanarwar Amurka da aka yi a jiya, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce, kasarsa na da burin warware batun nukiliyar Koriya ta Arewa ta hanyar diplomasiyya. Amurka na son tattaunawa da mahukuntan Koriya ta Arewa ba tare da gindaya wani sharadi ba, da zarar mahukuntan Pyongyang sun shirya yin haka. (Tasallah Yuan)