Cikin jawabin na sa, shugaba Xi Jinping ya yi maraba da zuwan shugaba Moon Jae-in kasar Sin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Koriya ta Kudu.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin da Koriya ta Kudu abokan hadin gwiwa ne dake makwabtaka da juna. Ya ce a cikin shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, an samu babban ci gaba kan hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, matakin da ya kawo moriya gare su.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin na maraba da kasar Koriya ta Kudu da ya shiga aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", tare da fatan za a hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da manufofin raya kasar Koriya ta Kudu, da kokarin neman tsarin hadin gwiwa na samun moriyar juna, ta haka za a samu bunkasuwa tare.
A nasa bangare, shugaba Moon Jae-in ya bayyana cewa, wannan ne karo na 5 da ya kawo ziyara nan kasar Sin, ya kuma yabawa nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa mai dorewa. Ya ce kasar Koriya ta Kudu tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara yin imani da juna a fannin siyasa, da sada zumunta a tsakanin jama'arsu, da kara yin mu'amala da juna, da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da sa kaimi ga samun sabon ci gaba bisa tushen samun moriyar juna, da inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)