Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, kasarsa da Koriya da Kudu za su ci gaba da karfafa yin tattaunawa da hadin gwiwa domin tabbatar da zaman lafiya da hana barkewar yake-yake a zirin Koriya.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin da ke zantawa da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in yau Alhamis wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin tun daga jiya har zuwa ranar 16 ga wata, ya ce kasashen biyu suna da muradu iri daya game da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin na Koriya.