Yau Talata 2 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru cewa, za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, wato FOCAC a nan kasar Sin, inda shugabannin Sin da Afirka za su taru a nan Beijing domin tattauna manufofin yin hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin bangarorin 2, da tsara yadda za a inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a sabon zamani, a kokarin tabbatar da samun nasara da bunkasuwa tare matuka.
A ranar 1 ga wata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma suka aikawa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen 2. A cikin sakonsa, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin za ta shirya taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a bana. (Tasallah Yuan)