Jami'in ya fadi haka ne a wajen taron hada hadar zuba jari, da raya tattalin arziki a fannin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", wanda ya gudana jiya a nan birnin Beijing. Cikin jawabin da ya gabatar wajen taron, Wang ya ce, kungiyar 'yan kasuwa masu zaman kansu ta Sin da Afirka, za ta hada kai tare da sauran hukumomi na kasar Sin, domin gudanar da wasu ayyuka na binciken yanayin kasuwanni a kasashen Afirka.
Sa'an nan kungiyar za ta taimakawa kamfanonin hada-hadar kudi na kasar Sin, domin su kara zuba jari a nahiyar Afirka, musamman ma a yankuna na masana'antu da kasar Sin ta gina wa kasashen Afirka. Har ila yau, kungiyar za ta kara kafa cibiyoyin horaswa a wasu kasashen dake nahiyar Afirka, don samun karin ma'aikata masu kwarewa. (Bello Wang)