Xi Jinping ya yi nuni da cewa, wannan taro muhimmin mataki ne da bangarorin Sin da Afirka suka dauka, wajen sa kaimi ga aiwatar da sakamakon taron kolin Johannesburg na FOCAC, kana yana taimakawa wajen raya hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Gudanar wannan taro a cewar shugaba Xi ya shaidawa kasashen duniya cewa, Sin da Afirka na bunkasa hadin gwiwa, da samun moriyar juna duk da sauyin yanayin duniya da ake fuskantar. Kaza lika Sin na ci gaba da nuna goyon baya ga sha'anin shimfida zaman lafiya, da samun bunkasuwar nahiyar Afirka. (Zainab)