Wang Yi: ana kokarin bullo da sabon tsarin hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da Afirka
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyanawa 'yan jarida yayin da yake halartar taron masu shiga-tsakani kan sakamakon taron kolin Johannesburg na FOCAC yau a nan birnin Beijing cewa, taron na wannan karo ya zarce yadda aka zata a baya, ministoci da manyan jami'ai fiye da 100 daga kasashen Afirka ne suka halarci taron, wanda ya kasance gagarumin taro na hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Wannan ya shaida cewa, sabon tunanin hadin gwiwar Sin da Afirka musamman shirye-shirye 10 na hadin gwiwa tsakanin sassan biyu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron kolin Johannesburg na FOCAC sun dace da bukatun kasashen Afirka, wadanda suka samu karbuwa sosai a kasashen Afirka. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku