A wannan rana, Mr. Kairuki ya ba da jawabi mai taken "Hadin gwiwar Sin da Afirka: yadda ake fata da kuma yadda ake aiwatarwa" a yayin taron tattalin arziki da sha'anin kudi na Caixin da aka yi a birnin Beijing. Ya ce, a halin yanzu, ana samar da wutar lantarki ga yankuna kashi 38 bisa dari a fadin nahiyar Afirka, yayin da ake samar da hidimar amfani da yanar gizo da ba ta wuce kashi 10 bisa dari a nahiyar ba, lamarin da ke haifar da ja bayan bunkasuwar harkokin masana'antu a Afirka.
Hakan a cewar sa shi ne dalilin fatansa, na ganin za a mai da hankali kan wadannan batutuwa a yayin taron FOCAC karo na 7, domin taimakawa kasashen nahiyar wajen gaggauta yunkurin raya harkokin masana'antu. (Maryam)