Wang Yi ya bayyana cewa, sabon tunani da sabbin matakai da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron kolin Johannesburg na FOCAC sun canja zuwa sakamakon amfanawa jama'ar Sin da Afirka da yawansu ya kai biliyan 2 da miliyan 400. Sin ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su zabi hanyoyin samun bunkasuwa masu dacewa da yanayinsu, kana tana son yin kokari tare da kasashen Afirka wajen kara yin imani da juna a fannin siyasa da kirkiro hanyoyin hadin gwiwa na samun moriyar juna, ta haka za a iya taimakawa kasashen Afirka wajen inganta karfinsu na samun ci gaba da kansu da kuma samun zaman lafiya da bunkasuwa mai dorewa.
Bangaren Afirka ya nuna yabo ga kasar Sin domin ta yi kira da a gudanar da taron masu shiga-tsakani na taron kolin Johannesburg na FOCAC, kana sun nuna gamsuwa ga aikin aiwatar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka. Ministocin kasashen Afirka sun nuna yabo ga raya dangantakar dake tsakaninsa da kasar Sin, suna son yin kokari tare da kasar Sin wajen zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna da sada zumunta, da inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. Kana ministocin sun nuna goyon baya ga matsayin Sin kan batun tekun kudancin kasar Sin, suna son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin don tabbatar da samun moriyar juna. (Zainab)