in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka yadda ya kamata
2016-07-29 16:28:35 cri

A gun taron kolin Johannesburg na FOCAC da aka gudanar a karshen shekarar bara, an daga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, tare da gabatar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwarsu.

A kuma Juma'ar nan ne aka gudanar da taron masu shiga-tsakani, kan sakamakon taron kolin Johannesburg na FOCAC a nan birnin Beijing. A gun bikin bude taron, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, taron kolin Johannesburg ya bude sabon shafi na hadin gwiwa, da samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka.

A rabin shekara da ta gabata, an samu babban ci gaba wajen aiwatar da sakamakon taron.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, an daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa 243, wadanda suka shafi kudin Amurka dala biliyan 50.725. A cikinsu, yawan jarin da kamfanonin Sin ta zuba wa kasashen Afirka kai tsaye, da rancen kudin da Sin ta bayar domin yin ciniki, ya zarce dala biliyan 46. Ana samun kyakkyawan yanayi wajen hadin gwiwar samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka, matakin da ya shaida kyakkyawar makomar hadin gwiwar sassan biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China