in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta cimma nasarar yaki da ta'addanci a Syria
2017-12-28 12:16:53 cri

A farkon watan Disamba bana, shugaban kasar Rasha ya sanar da kammala aikin yaki da ta'addanci a kasar Syria, sa'an nan, ya ziyarci sansanin sojojinsa na sama na Hemeimeem dake kasar Syria, inda ya ba da umurnin fara janye sojojin Rasha daga Syria.

Lamarin da ya nuna cewa, bayan shekaru 6 da dukufa wajen yaki da ta'addanci, a halin yanzu, an kusan kawo karshensa a kasar ta Syria baki daya. Haka kuma, kasar Rasha ta cimma nasarar karfafa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Syria, Turkiya da Masar, yayin da take inganta tasirinta a yankin Gabas ta tsakiya.

Dangane da wannan batu, ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

A ranar 11 ga watan Disamba, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kai ziyara a sansanin sojojin sama na Hemeimeem dake kasar Syria, inda ya ba da jawabi cewa, kasar Rasha za ta janye galibin sojojinta daga kasar Syria.

"Cikin shekaru biyu da suka gabata, sojojin kasar Rasha da sojojin kasar Syria sun cimma nasasar yaki da kungiyar ta'addanci mafi karfi a duk fadin duniya cikin hadin gwiwa, shi ya sa, a yanzu na tsai da kuduri cewa, za a janye galibin sojojin kasarmu daga Syria. Kuma, an riga na ba da umurni ga ministan harkokin tsaron kasa, da babban hafsan rundunar sojojin kasar mu, da su fara aiwatar da janye sojojin Rasha daga kasar Syria."

Bugu da kari, shugaba Putin ya jaddada cewa, za a ci gaba da rike sansanin sojojin sama na Hmeymim, da kuma sansanin sojojin teku na Tartus na kasar Rasha dake kasar Syria, domin kandagarkin farfadowar ta'addanci a kasar. Wato a duk lokacin da aka samu wata tarzoma, sojojin kasar Rasha za su iya mai da martani gare su da babban karfi irin wanda ba a taba gani ba.

Kafin haka kuma, ma'aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta taba sanar da cimma nasarar 'yantar da dukkan birane da matsaugunin 'yan kasar Syria daga hannun kungiyar ta'addanci.

A nasa bangare kuma, shugaban hukumar kula da harkokin yake-yake ta hedkwatar ba da nasiha ga rundunar sojan kasa ta Rasha Sergey Rudskoy ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, sojojin kasar Rasha sun riga sun kammala ayyukansu na yaki da ta'addanci a kasar Syria.

"A karshe, rundunar sojojin kasar Rasha ta karfafa matakan sojanta ta sama, a ko wace rana, jiragen sojan sama na tashi har sau dari daya domin kai wa 'yan ta'addda hare-hare, inda suka cimma nasarar lalata sansanonin 'yan ta'adda da gidajen ajiye makaman su da dama, haka kuma, an yi amfani da jiragen saman yaki mai jefa boma-bomai, da kuma mai cin dogon zango da dama a aikin daukar matakan soja."

Bugu da kari, shugaba mai kula da harkokin Gabas ta Tsakiya na cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Rasha Vladimir Fitin ya bayyana cewa, a shekarar 2017, babban sakamakon da kasar Rasha ta cimma a kasar Syria shi ne, cimma nasarar yaki da manyan dakarun kungiyar IS. Sojojin gwamnatin sun kuma 'yantar da manyan birane a kasar, ciki har da birnin Aleppo da kuma birnin Deir el-Zour da dai sauransu.

"Idan muka yi tsokaci kan moriyar Rasha, za a gane cewa, mun halaka 'yan ta'addan da mai yiwuwa ne su dawo kasar Rasha suna kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasar. Ban da haka kuma, an nunawa al'ummomin kasa da kasa cewar, muna da karfin yaki da 'yan ta'adda, da kuma cimma nasarar yaki da su, wannan na da muhimmiyar ma'ana. Haka kuma, babbar gudummawar da kasar Rasha ta bayar kan wannan aiki ta karfafa tasirin kasar a kasashen Larabawa."

A watan Janairu na shekarar bana, an yi taron neman sulhu na Astana bisa hadin gwiwar kasashen Rasha da Turkiya da Iran, lamarin da ya yi amfani kwarai wajen warware matsalar siyasa a kasar Syria, yayin da ake ba da gudummawa ta gudanar da taron neman sulhu na Geneva cikin yanayi mai kyau.

Haka zalika, bayan watanni da dama, an gudanar da taron neman sulhu na Astana sau da dama, inda aka tattauna kan batun tsagaita bude wuta, da kafa kwamitin neman sulhu a tsakanin kabilun kasar Syria, yayin da ake kulla yarjejeniyoyin masu alaka da hakan masu yawa.

Dangane da wannan lamari, Vladimir Fitin ya nuna cewa, a lokacin da aka kusan kawo karshen matakan soja a kasar Syria, an shiga wani sabon matsayi kan aikin neman sulhu a kasar Syria, lamarin da ya kasance wani sabon kalubale ga kasar Rasha wajen karfafa tasirin siyasarta a yankin.  

"A halin yanzu, kasar Syria na bin hanyarta ta neman sulhu, da kuma gina zamantakewar al'umma cikin zaman lafiya. Kasar Rasha ta ba da babbar gudummawa kan wannan batu, ciki har da inganta yunkurin shawarwarin neman sulhu na Astana. Haka kuma, kasar Turkiya da kasar Iran sun yi hadin gwiwa da kasar Rasha, wajen dawo da bangarori daban daban na kasar Syria kan teburin yin shawarwari, domin nazartar harkokin gyara tsarin mulkin kasa, da kuma gudanar da babban zaben kasar cikin 'yancin kai, wadannan sun kasance manyan batutuwa guba biyu dake kan gada ga kasar Syria a halin yanzu."(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China