in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala sabon zagayen tattaunawar neman sulhu a Syria ba tare da cimma wata kwakkwarar yarjejeniya ba
2017-12-15 13:54:59 cri

Manzon musammam na MDD kan rikicin Syria Staffan de Mistura, ya ce an kammala zagaye na 8 na tattauanwar neman sulhu a Syria ba tare da cimma wata yarjejeniya mai kwari ba.

Ya ce duk da dimbin kokarin da aka yi, ba a cimma wata yarjejniya mai ma'ana ba, kuma ba a tattauna da wakilan gwamnatin Syria ba, game da maudu'an kundin tsarin mulki da na zabe karkashin kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhu na MDD, yana mai cewa an yi rashin kyakkyawar dama.

Manzon na musammam wanda ya ce kafin ci gaba da tattaunawar, sai ya kai rahoto ga kwamitin sulhun a birnin New York, ya ce babu wata mafita face samun amincewar MDD.

Zai kuma nemi shawarar jakadun musamman daga kasashe mambobin din-din-din na kwamitin, wadanda dama su yake tuntuba.

Staffan de Mistura ya ce bangarorin 2, wato na gwamnati da 'yan adawa na zargin juna da shimfida sharruda kafin cimma matsaya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China