A jiya ne, Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kasar Sudan ta Kudu tana cikin wani hali mai sarkakkiya. Abin da ya dace a yi yanzu shi ne ci gaba da gaggauta kara sulhuntawa a kasar ta Sudan ta Kudu ta fuskar siyasa tare da samar da kwanciyar hankali a kasar.
A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro domin nazarin halin da ake ciki a Sudan ta Kudu. A cikin jawabinsa, Liu Jieyi ya bayyana fatansa na ganin kungiyoyin shiyya-shiyya sun ci gaba da tuntubar gwamnatin Sudan ta Kudu, tare da bayyana ra'ayoyinsu da murya daya, a kokarin yin hadin gwiwa ta fuskar siyasa. (Tasallah Yuan)