in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: aikin shimfida zaman lafiya a Sudan ta Kudu na tafiyar hawainiya
2017-09-27 19:05:02 cri
Manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Sudan ta Kudu, David Shearer, ya gabatar da wani rahoto ga kwamitin sulhu na majalisar, a jiya Talata, kan yanayin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki, inda ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar hawainiya a yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar.

A cewar Shearer, bangarorin kasar da ba sa ga maciji da juna ba sa nuna cikakken saukin kai, yayin da ake neman aiwatar da yarjejeniyar sulhu da aka kulla a shekarar 2015. Haka zalika, ba sa nuna matukar sha'awa ga gudanar da shawarwarin.

Har ila yau, Shearer ya nuna damuwa kan yanayin aikin jin kai a Sudan ta Kudu. A cewarsa, mutane fiye da miliyan 7.6 na bukatar tallafi, wanda rashinsa zai jefa jama'ar kasar da yawa cikin mawuyacin hali.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China