in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A shirye UNMISS yake ya warware sabanin Sudan ta Kudu idan aka bukace shi
2017-11-10 13:04:18 cri

Rundunar wanzar da zaman lafiya da MDD ta tura a kasar Sudan ta Kudu UNMISS, ta ce a shirye take, ta ba da taimako wajen warware sabanin dake tsakanin Gwamnatin kasar da tsohon babban hafsan rundunar SPLA Paul Malong idan aka bukace ta.

Kakakin rundunar UNMISS Daniel Dickinson, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rundunar na ganin sabanin a matsayin harka ta cikin gida, amma a shirye take ta taimaka idan dukkan bangororin suka nema.

Ya kara da cewa, duk da cewa batu ne na cikin gida ga al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu, rundunar na kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki su warware takaddamar cikin ruwan sanyi.

An yi wa Janar Malong daurin talala, bayan an sallame shi daga aiki a watan Mayu, saboda kin biyayya ga umarnin shugaba Salva Kiir da ya nemi ya rage kimanin 30 daga cikin dogarawansa ya bar guda 3. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China