in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa a harkokin gudanarwar duniya karkashin tsarin MDD
2017-12-20 15:16:48 cri

Wani kwararren jami'in MDD ya bayyana cewa, kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa da kuma ba da babbar gudunmowa game da tafiyar da al'amuran da suka shafi ci gaban kasa da kasa ta hanyar amfani da tsarin MDD, kasancewar manufofin gwamnatin Sin sun yi daidai da manufofin MDDr.

Abdelkader Abbadi, wani marubuci kuma kwararren jami'in MDD wanda ya shafe shekaru 50 yana aiki a helkwatar MDDr ya bayyana cewa, shawarar shugaba Xi Jinping na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama, ta yi daidai da ajandar MDD, wadda ta baiwa bunkasa ci gaba da wanzar da zaman lafiya fifiko.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana taka rawar a-zo-a-gani wajen wanzar da zaman lafiyar duniya, musamman duba da irin yadda take sake zamanantar da manufofinta na lafiya da kwanciyar hankali da kuma kyakkyawar makwabta.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China