Karuwar tattalin arzikin duniya na baya bayan nan yafi karfi ne daga bangaren manyan kasashen mafiya karfin tattalin arziki, ko da yake, kasashen gabashi da kudancin Asiya su ne yankunan da suka fi samun sauyi mafi yawa.
Kawo karshen matsin tattalin arziki a kasashen Argentina, Brazil, Najeriya da Russia, hakan ya taimaka matuka wajen karuwar tattalin arzikin duniya tsakanin shekarun 2016 da 2017, kuma wannan ya taimaka wajen bunkasuwar cinikayya a duniya da kuma inganta yanayin zuba jari.
Yayin kaddamar da rahoton, mataimakin sakataren janar mai kula da al'amurran tattalin arziki da walwala na MDD Liu Zhenmin ya lura cewa, bunkasuwar tattalin azrikin duniyar da aka samu alamun ne dake nuna samun makoma mai kyau ga tattalin arzikin duniyar, sai dai yana da muhimmanci a tuna da yanayin da muhalli ke ciki a duniya in ji shi. A cewarsa wannan ya nuna bukatar dake akwai na hada karfi da karfe wajen gwama cigaban tattalin arziki da kuma batun shawo kan gurbatar muhalli.(Ahmad Fagam)